
In his unrelenting effort to proactively respond to the global pandemic, Coronavirus, the Kano state governor Dr Abdullahi Umar Ganduje holds live state broadcast today Monday, March 23, 2020, by 2pm.
The state-owned Radio Kano and Abubakar Rimi Television (ARTV) and some local radio stations will have live broadcast by the governor.
He will give details of the situation at hand in the state and other efforts of the state government in responding to the threat of the menace.
While calling for individual personal hygiene, as amplified by health workers, would be reiterated by the governor, he would also urge for public support of the recently instituted State Task Force on COVID-19.
Abba Anwar
Chief Press Secretary to the Governor of Kano State
Monday, March 23, 2020
[email protected]
Sanarwa Ta Musamman
Cutar “Coronavirus” : Gwamnan Kano Ganduje Zai Jawabi Kai Tsaye Ga Jama’a Ta Kafafen Yada Labarai Yau Litinin Da Karfe 2 Na Rana
Yau ne kafafen yada labarai mallakin gwamnatin jihar Kano, wato gidan Talabijin na Abubakar Rimi (ARTV) da gidan Rediyon Jihar Kano da wasu tashoshin Rediyo Masu Zaman Kansu, za su jona jawabi na musamman da Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai wa jama’ar Kano, kan wannan cutar da ta zama annoba ga duniya ta “Coronavirus ko COVID-19.”
Wannan duk ya na cikin irin kokarin shirin ko-ta-kwana da gwamnatin Gandujen ke yi ne wajen fuskantar wata barazana da ka iya tasowa dalilin wannan annoba, wadda ta zamewa duniya alakakai.
Shi Gwamnan a cikin jawabinsa zai fadi shirin da gwamnatinsa ke ciki tare da neman hadin kan jama’a ga jami’an kiwon lafiya game da shawararin da suke bayarwa don neman gujewa wannan balahira. Game da rokon jama’a da su kasance masu tsaftar kansu da kansu don gujewa fadawa halakar annobar.
Abba Anwar
Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano
Litinin, 23 ga Watan Maris, 2020
[email protected]
